An kama ɓarayin waya 35 a Kaduna

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama mutane 35 da ake zarginsu da ƙwacen waya a yayin wani samame da suka kai wasu matattarar ɓatagari dake cikin kwaryar birnin jihar.

A wata sanarwa ranar Asabar, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Mansur Hassan ya ce sashen rundunar dake yaƙi da miyagun laifuka shi ne ya ƙaddamar da samamen domin daƙile ƙaruwar yawan satar waya da ake samu a jihar.

A cewar sanarwar” An kai samamen a tsakanin ƙarfe 07:00 zuwa 11:45 na daren kowace rana daga ranar Talata zuwa Juma’a bisa umarnin da kwamishinan ƴan sanda, Aliu Dabigi ya bayar,”

“An samu mutanen da ake zargi ɗauke da muggan makamai, tabar wiwi da kuma wasu haramtattun kwayoyi.”

Hassan ya ce duk wanda aka samu da laifi a cikin mutanen za a gurfanar da shi a gaban kotu.

More from this stream

Recomended