
An ji ƙarar fashewar wani abu da ake kyautata nakiya ce akan babban bututun mai na Trans Niger Pipeline dake garin Bodo a ƙaramar hukumar Gokana ta jihar Rivers.
Lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Litinin a kusa da titin Bodo-Bonny da ake aikin ginawa.
Daga hoton fefan bidiyo da aka fara watsawa da safiyar ranar Talata ana iya ganin wuta naci ganga-ganga da kuma hayaki da ya turnuke sararin samaniya a wurin da aka tashi nakiyar.
Kawo yanzu dai ba za iya tabbatarwa ba ko fasa bututun na da alaƙa da barazanar da wasu kungiyoyin tsagerun yankin Neja Delta suka yi na fara fasa bututun mai kan rikicin siyasar jihar Rivers.