An dage hawan sallah a Katsina saboda kashe-kashe

Shugaba Buhari da sarkin Katsina
Image caption

Fadar masarautar Katsina ta fitar da wata sanarwar a jiya, wadda a ciki ta aike sakon jaje ga daukacin jama’arta kan ibtila’in kashe-kashen da mutanen gundumomin Batsari, da Dan-Musa, da Kankara sa Wagini da sauransu wuraren da abun ya shafa suka samu kansu a ciki.

Sakataren masarautar Alhaji Bello M IFO shi ne ya fitar da ita, tare da shaidawa jama’a ce wa sakamakon halin da suka samu kansu a ciki na alhiji da jimami masarautar ta yanke shawarar a wannan karon ba za a yi hawan sallah kamar yadda aka saba ba.

Alhaji Bello ya ce Mai-martab sarkin Katsina Dr Alhaji Abdulmumin Kabir Usman CFR da majalisar masarautar ne suka ga dacewar dage duk wasu shagulgula dan nuna alhini kan abin da ya samu jama’arsu.

A karshen sanarwar ta ce za a je sallar Idi kamar yadda aka saba, da yin addu’o’in neman zaman lafiya ga jihar Katsina da Najeriya baki daya.

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...