Al-makura ya lashe tikitin APC na takarar sanata

Gwamnan jihar Nasarawa,Umar Tanko Al-makura ya lashe tikitin jam’iyar APC na takarar sanata a mazabar Nasarawa ta kudu.

Shugaban kwamitin zaben Isamila Ahmed wanda ya samu wakilcin sakataren kwamitin, Ahmed Candido shine ya sanar da sakamakon zaben ranar Laraba a Lafiya.

Ahmed ya ce Al-makura ya lashe zaben da kuri’a 1,262 ya yin da abokin takararsa Salisu Egyegbola ya samu ƙuri’u 312.

Ya ce wakilai 1612 aka sa ran za su kada kuri’a a zaben amma 1608 aka tantance ya yin da 1594 suka kada kuri’a.

Haka kuma Al-makura ya bayyana farin cikinsa da sakamakon zaben inda ya sadaukar da nasarar da ya samu ga mutanen jihar.

Ya kuma yaba da daddakon da abokin takararsa ya nuna kan yadda ya karbi sakamakon zaben da kyakkyawar zuciya.

Gwamnan ya yi alkawarin ba zai bawa al’umma kunya ba matukar suka zabe shi a matsayin sanata mai wakiltar mazabar Nasarawa ta kudu a zabe mai zuwa.

More News

Tinubu zai wuce Paris daga London

Shugaba Bola Tinubu na shirin zuwa birnin Paris na kasar Faransa daga birnin Landan na kasar Birtaniya, a kowane lokaci daga yanzu don wani...

Gwamnan Kano ya bawa ƴan kasuwar Kantin Kwari da gobara ta shafa tallafin miliyan ₦100

Gwamnan jihar Kano,Abba Kabir Yusuf ya sanar da bada tallafin kuɗi miliyan ₦100 a madadin gwamnatin Kano ga mutanen da iftila'in gobara ya faɗawa...

Gwamnatin Katsina za ta samar da kantunan Rumbun Sauki

Gwamnatin jihar Katsina ta shirya tsaf domin fara aiwatar da wani tsari na sayar da kayan amfanin yau da kullum akan farashi mai rahusa. Sabon...

Ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta buƙaci a koma sayar da fetur a tsohon farashin lokacin Buhari

Ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta koma sayar da mai a tsohon farashin kuɗin mai na watan Yunin...