Abacha ya yaudari ‘yan siyasa – IBB

Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Sani Abacha, wanda ya mulki kasar daga 1993 har lokacin mutuwarsa a 1998, ya hau mulkin ne bayan ya yaudari ‘yan siyasa, a cewar Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Janar Babangida ya bayyana haka ne a hirarsa da Trust TV

, yayin da yake bayyana yadda Abacha ya yi yaudari mutane ya kwace mulki.

Abacha, wanda IBB ya bayyana a matsayin “babban abokina”, ya kasance hafsan hafsoshin sojoji a lokacin mulkin Babangida daga 1985, kuma daga baya ya nada shi Ministan Tsaro a 1990.

Babangida ya ce, gwamnatin Abacha tana da wayo. Sun san wadanda suka fi magana a kan zabe da juyin mulkin da batun 12 ga watan Yuni da sauran abubuwa.

Sai suka fara magana da su, suka yaudare su da karfafa musu guiwa su kawar da gwamnatin rikon-kwarya, da cewar idan sun kawar da gwamnatin rikon-kwaryar, za su dawo da su, su ba su abin da suke so mulkin dumokuradiyya, daga nan sai a kafa gwamnatin farar hula.

Babangida ya ce: ”Da wannan suka yaudari jama’a da sauran fitattun mutane, saboda haka da Abacha ya shigo, sai ake ta murna, hankali ya kwanta; Madalla abu ya yi kyau! Abin da zai faru a gaba kuma shi ne zababbiyar gwamnatin dumokuradiyya. Ni na sani, mun sani, hakan ba zai yiwu ba saboda maganar ita ce: (Abacha zai ce ), Me zai sa in sa kaina cikin hadari, kawai in zo in danka muku mulki?’ Wannan shi ne abin da ya faru.” In ji Babangida.

More News

2023: 7 APC aspirants battling for Oyo central senatorial district ticket

No fewer than seven aspirants on the platform of the All Progressives Congress (APC), have indicated interest to represent Oyo Central senatorial district in...

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...

Sojojin sun kama tarin makamai a a hannun mayakan IPOB

Rundunar sojan Najeriya ta samu nasarar kama makamai da suka hada bindigogi hodar hada bam a jihar. Rundunar ta samu gagarumin wannan nasara ne biyo...