Rundunar Sojin Sama Ta Najeriya Ta Yi Ayyukan Tsaro 2,900, Ta Ƙone Litar Man Jirgi Miliyan 10

Muhammadu SabiuHausa10 minutes ago



Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta gudanar da ayyukan zirga-zirgar jiragen sama sama da 2,900, inda ta shafe sa’o’i 6,100 tana tashi tare da amfani da kusan litar man jirgin sama miliyan 10 tsakanin Nuwamba 2025 da Satumba 2026, a wani ɓangare na ayyukan tabbatar da tsaron ƙasa.

Daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai na rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, gabanin cikar shekara ɗaya da Air Marshal Sunday Aneke ya yi a matsayin Babban Hafsan Sojin Sama, ranar 30 ga Oktoba.

Ya ce ayyukan sun haɗa da hare-haren sama masu nufin kai hari daidai inda ake buƙata, sintiri mai ɗauke da makamai, sa ido da kuma taimaka wa dakarun ƙasa daga sama, domin raunana abokan gaba da inganta ayyukan jami’an tsaro.

Ejodame ya bayyana cewa an tsara ayyukan ne bisa sahihan bayanan sirri, tare da fayyace manufofin kowane aiki da tantance sakamakonsa, domin tabbatar da cewa kowace tafiyar jirgi tana da amfani ga tsaron ƙasa.

Dangane da walwalar jami’ai, ya ce rundunar ta ɗauki matakan inganta alawus, kiwon lafiya, masauki da sauran kayayyakin more rayuwa. Haka kuma, an sake farfaɗo da zirga-zirgar jiragen da ake amfani da su wajen jigilar jami’an da ke bakin daga.

Ya bayyana cewa an ɗaga manyan hafsoshi 57 zuwa mukaman Air Vice Marshal da Air Commodore. Haka kuma, manyan jami’an da ba hafsoshi ba 1,534 da sauran jami’ai 1,936 sun samu ƙarin girma. Fiye da jami’ai 550 sun halarci horo da shirye-shiryen ƙwarewa a ƙasashen waje, yayin da sama da 6,000 suka samu horo a cikin gida.

A ɓangaren sabunta jiragen yaƙi, rundunar ta karɓi ƙarin jirage masu saukar ungulu guda biyar a watan Satumba, waɗanda suka haɗa da AW-109 Trekker Type B guda uku da H125 guda biyu. Rundunar ta kuma ce tana shirin sayen jiragen yaƙi masu saukar ungulu samfurin AH-1Z guda 12, da sauran jiragen sama da na’ura marasa matuƙi domin ƙarfafa ƙarfin yaƙi, sa ido da tattara bayanan sirri.

Sanarwar ta ƙara da cewa ana gyarawa da inganta jiragen L-39ZA guda shida a Slovakia da Najeriya, yayin da ake gudanar da babban aikin gyaran jirgin jigilar kaya na C-130 a Portugal.

A fannin kayayyakin more rayuwa, rundunar ta amince da ayyuka 284, inda aka kammala 145, yayin da sauran 139 ke ci gaba da gudana. Ayyukan sun shafi gidajen zama, makarantu, cibiyoyin lafiya, hanyoyi, wutar lantarki, samar da ruwa da gine-ginen gudanarwa.

Rundunar ta kuma ce tana ƙarfafa tsarin kiyaye lafiyar zirga-zirgar jiragen sama, gudanar da binciken tsaro da kuma samar da hanyoyin rage illolin da ayyukan soji za su iya haifar wa fararen hula.

A ƙarshe, Ejodame ya ce rundunar za ta ci gaba da amfani da jarin da ake kashewa wajen horar da jami’ai, sayen jirage, inganta fasaha da gine-gine domin ƙara ingancin ayyukan tsaro da tunkarar matsalolin tsaron da Najeriya ke fuskanta.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...