

Wasu da ake zargin cewa masu garkuwa da mutane ne sun sace Shugaban matasan jam’iyyar APC na mazabar Ogbabede da ke gundumar Abocho a Karamar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi, Mista Arome Adaji, da matarsa, Misis Justina Arome, daga gidansu.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na daren ranar Laraba, lokacin da wasu dauke da makamai suka kai farmaki gidansu da ke kan titin Ajegwuna a Abocho.
A cewar wasu bayanai daga al’ummar yankin, maharan sun rika harba bindigogi ba ƙakkautawa yayin da suka shiga titin, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin tserewa domin tsira kafin daga bisani su tafi da ma’auratan.
Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da Ndamodu ya ce Adaji, wanda aka fi sani da “Iron Gate”, da matarsa suna gida suna hutawa ne lokacin da aka fara jin karar harbe-harben bindiga a kusa da gidansu.
“Mr Arome Adaji, wanda aka fi sani da Iron Gate, da matarsa suna gida suna hutawa lokacin da kwatsam aka fara jin karar harbe-harben bindiga a kusa da gidansu.
“Karar harbe-harben ta tsoratar da mazauna yankin har suka kasa fitowa, domin babu wanda yake son fadawa cikin musayar wuta ko kuma harsashin da ya kauce wa hanya.
“Bayan masu garkuwar sun bar wurin ne mazauna yankin suka fito domin gano inda aka kai harin, sai suka fahimci cewa an yi awon gaba da shugaban matasan da matarsa,” a cewarsa.
Wani jagoran al’umma, Surveyor Agono Eneogba, ya ce masu dauke da makamai sun fara sauya salon hare-harensu daga manyan hanyoyi zuwa gidajen jama’a, gonaki da matsugunan manoma a sassan yankunan Kogi ta Gabas.
Ya ce:
“Jami’an tsaro, masu sintiri da kuma mafarauta na gargajiya sun tsaurara sanya ido a kan hanyoyin yankunan Kogi ta Gabas. Tsawon makwanni yanzu, masu aikata wadannan laifuka sun rage hare-hare a kan hanyoyi, suna mai da hankali kan gidaje da gonaki ko matsugunan manoma, inda suke yin garkuwa da mutane masu matukar yawa.”
Bayanin Eneogba ya zo ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin wasu karin sace-sacen mutane a yankin.
A ‘yan makonnin da suka gabata, an ruwaito cewa wasu dauke da makamai sun yi garkuwa da wata mata da ‘ya’yanta hudu yayin da suke dawowa daga wurin jana’iza a garin.
Rahotanni sun ce wadanda aka sace sun samu ‘yancinsu ne bayan an biya kudin fansa ga masu garkuwar.