Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta kawo ƙarshen matsalar ta’addanci da ’yan bindiga a faɗin ƙasar.
A saƙonsa na Babbar Sallah da ya fitar ranar Talata, Tinubu ya amince cewa hare-haren da ya kira na “’yan ta’adda da ’yan bindiga marasa tausayi” na ci gaba a wasu al’umma. Sai dai ya ce gwamnati ba ta yi watsi da waɗanda matsalar tsaro ta shafa ba.
Ya ce, “Za mu murƙushe dukkan miyagun ƙarfi a ƙarshe.”
Shugaban ya kuma kare manufofin tattalin arzikin gwamnatinsa, inda ya ce sauye-sauyen da aka aiwatar cikin shekaru uku da suka gabata sun fara haifar da sakamako mai kyau.
A cewarsa, “Tafiyar cikin duhun rami ta ƙare, yanzu haske ya bayyana.”
Tinubu ya ce an samu ci gaba a yaƙi da rashin tsaro, ciki har da kashe wani shugaban ISIS da hukumomi ke nema ruwa a jallo. Ya ƙara da cewa gyare-gyaren da ake yi a ɓangaren tsaro za su taimaka wajen samar da zaman lafiya da ƙarin damar tattalin arziki.
Haka kuma ya bayyana Babbar Sallah a matsayin lokaci na tunawa da muhimmancin imani, sadaukarwa, tausayi da haɗin kai, tare da kira ga Musulmi da su yi addu’ar zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Tinubu Ya Sha Alwashin Murƙushe ’Yan Ta’adda Da ’Yan Bindiga

