Hukumar NAFDAC ta bankado wuraren ajiya guda biyu da ke cike da magungunan da suka lalace a titin Sam Mbakwe, Aba da ke jihar Abuja.
Wasu daga cikin magungunan an sake liƙe musu sabon lakabin kwanan watan lalacewa kafin jami’an tsaro su isa wurin.
Haka nan a karamar hukumar Osisioma, hukumar ta kwace tan 140 na magungunan da suka lalace, baya ga wasu da aka kama a kasuwar Ariaria.
An kuma tattara samfurin magunguna 178 don gwaji.
NAFDAC ta sha alwashin ci gaba da yaki da safarar magungunan da ke barazana ga lafiya.