Jam’iyyar APC ta lashe zaben dukkanin kujerun ƙananan hukumomin jihar Kaduna 23 da kuma na kejerun kansilolin jihar.
Hajara Muhammad shugabar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kaduna ce ta sanar da sakamakon zaɓen.
Ta sanar da cewa biyo bayan tattara sakamakon zaɓen da jami’an tattara sakamako suka sanar a matakin ƙananan hukumomi 23 da kuma mazaɓu 255 kamar yadda doka ta tanadar saboda da haka ta sanar da cewa jam’iyar APC ta lashe zaben a kananan hukumomi 23 da kuma dukkanin mazaɓun jihar 255.
Tun da farko gwamnan jihar, Mallam Uba Sani ya bayyana gamsuwarsa kan yadda zaɓen yake gudana a faɗin jihar.
Sani ya bayyana haka ne lokacin da yake kaɗa kuri’arsa a akwatu na 047 dake Kawo.