10.3 C
London
Thursday, November 7, 2024
HomeHausaƳan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Date:

Related stories

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...
spot_imgspot_img

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama wani  riƙaƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 ƙirar gida guda 20.

A wata sanarwa ranar Juma’a mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ya ce wanda aka kama ɗin mai suna, Bitrus Gyang ya fito ne daga Barikin Ladi a jihar Filato kuma an kama shi a Buruku dake ƙaramar hukumar Igabi  ta jihar Kaduna.

Ya ce an kama Gyang ne a ranar Alhamis lokacin da jami’an tsaro suke gudanar da binciken ababen hawa da suka saba a gadar Buruku.

Mai magana da yawun rundunar ya bayyana cewa  a lokacin da Gyang yake amsa tambayoyi ya faɗi cewa yana safarar bindigogi kuma wannan ne karo na uku.

Hassan ya ƙara da cewa kwamshinan ƴan sandan jihar, Ali Dabagi ya yabawa jami’an ƴan sandan kan sadaukarwar da suka nuna.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories