Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce jami’anta sun samu nasara kama wasu bindigogi guda 55 da ba a kammala haɗasu ba a filin Jirgin Saman Murtala Muhammad dake Lagos.
Da yake magana a wurin wani taron manema labarai ranar Laraba shugaban hukumar ta kwastam, Adewale Adeniyi ya ce ƙunshin kayan da aka kama darajar su ta kai naira miliyan 270 kuma an kama su ne a ranar 19 ga watan Yuni.
A ranar 19 ga watan Yuni 2024 jami’an dake filin jirgin saman MM2 da aka jibge ƙofofin fita sun tabbatar da cewa a bincika komai biyo bayan bayanan sirri da suka samu kan bindigogin.
A yayin binciken ne aka gano wani ɓangare da ake tunanin na bindiga ne hakan ya sa aka ware ƙunshin kayan har ta kai ga an gano bindigogin da suka fito daga ƙasar Turkiyya.
Hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da hukumar ta ƙwace bindigogi 844 da aka shigo da su ta tashar jirgin ruwan Onne a jihar Rivers.