Nijar tana son sanin duk waɗanda suka mallaki bindigogi a faɗin ƙasar

Makamai

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun ce ‘yan ƙasar sun fara amsa kira, wajen kai bindigoginsu don yin rijista a ƙarƙashin wani shiri da aka ƙaddamar ranar Talata.

Shirin zai tabbatar da yin rijista ga ɗaukacin bindigogin da fararen hula suka mallaka ta hanyar ofishin ministan cikin gida da haɗin gwiwar hukumar yan sanda.

Muhukunta sun ce maƙasudin aikin shi ne yi wa bindigogin lamba don sanin taƙamaiman adadin kayan harbin da ke hannun ‘yan ƙasar, da kuma tantance masu riƙe da bindigogi da izinin gwamnati a illahirin Nijar.

Ba su dai bayyana tsawon lokacin da za a kwashe ana aikin yi wa bindigogin lamba tare da tantance masu riƙe da su da izinin hukumomin ƙasar ba.

Nijar, na cikin ƙasashen Sahel masu fama da rikicin ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi irinsu Boko Haram da gungun masu fasa-ƙwaurin haramtattun kayayyaki ciki har da miyagun ƙwayoyi da makamai.

Masharhanta sun yi ta bayyana damuwa kan fantsamar makamai da bindigogi ta ƙasashe masu makwabtaka da Libya, kamar Jamhuriyar Nijar a faɗin yankin Sahel tun bayan faɗuwar gwamnatin Moammar Gaddafi a 2012.

Nijar ta ce shirin na da burin taimakawa wajen shawo kan matsalar yaduwar bindigogi tsakanin al’umma a faɗin ƙasar, matsalar da aka yi imani tana ta’azzara matsalar tsaro.

Kamfanin da Nijar ta damƙa wa alhakin gudanar da wannan gagarumin aiki ya ce sun ƙaddamar da shirin ne a Niamey, babban birnin ƙasar, kafin faɗaɗa shi zuwa sauran jihohi.

Jami’in kula da ayyuka na kamfanin SONIMA, Karimoun Albert Paul ya ce zuwa yanzu mutane sun amsa kira.

Shi ma wani ɗan Nijar da ya mallaki bindiga, kuma ya kai ta don yin rijista ya yaba da wannan tsari. Mutumin wanda bai yarda a ambaci sunansa ba, ya ce shirin zai ƙarfafa gwiwa kuma su samu kwanciyar hankali saboda a yanzu sun cika ƙa’idar malakar makami kuma riƙe da shi bisa izinin mahukunta.

Haka zalika, shugaban ƙungiyar masu sana’ar sayar da bindigogi a Nijar, Moussa Ahmed ya ce suna goyon bayan wannan shiri, da zai kawo ƙarshen mallakar bindigogi ta haramtacciyar hanya.

A cewar SONIMA daga ƙaddamar da shirin zuwa yanzu, kamfanin ya yi wa bindigogi kusan 800 lamba.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...