Hukumar EFCC shiyyar Ibadan ta yi wani kame na mutane 10 da suke rakiyar tireloli uku dauke da ma’adinan ‘Lithium’ da aka hako su ta haramtacciyar hanya.
Ana amfani da ma’adanan Lithium wajen hada jiragen sama da batura da magunguna da kuma sauransu.
Kakakin hukumar EFCC, Mista Dele Oyewale ya sanar cewa bayan daukar matakin bin sawu da jami’an hukumar suka yi, sun yi nasarar kama wadannan mutane da motocin a yankin Ogbomoso a Jihar Oyo.
Cikin sanarwar, Oyewale ya ce har zuwa lokacin da aka yi wannan kame, ba a iya gano ainihin inda mutanen suka yi nufin zuwa da wannan nau’in ma’adinin Lithium da aka loda su cikin manyan motocin ba.