Shugabar matan jam’iyar NNPP ta Shiyar Arewa Maso Yamma, Aisha Ahmad Kaita ta sauka daga muƙaminta.
A’isha wacce ta sanar da sauka daga muƙaminta a yayin wani taron manema labarai a Kano ranar Talata ta ce ta sauka daga muƙaminta ne a ƙashin kanta kuma za ta cigaba da zama a jam’iyar ta NNPP.
Ta ƙara da cewa matakin da ta ɗauka na da alaƙa kan yadda aka ƙi bawa mutanenta muƙami a gwamnatin Kano tun bayan da aka kafa gwamnatin.
Ta kuma bayyana biyayya ta ga jagoran jam’iyar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
A ƴan kwanakin nan dai ƴaƴan jam’iyar ta NNPP na cigaba da nuna rashin jin daɗinsu kan yadda aka yi watsi da su tun bayan kafa gwamnati.