Shugabar Matar Jam’iyar NNPP A Arewa Maso Yamma Ta Yi Murabus

Shugabar matan jam’iyar NNPP ta Shiyar Arewa Maso Yamma, Aisha Ahmad Kaita ta sauka daga muƙaminta.

A’isha wacce ta sanar da sauka daga muƙaminta  a yayin wani taron manema labarai a Kano ranar Talata ta ce ta sauka daga muƙaminta ne a ƙashin kanta kuma za ta cigaba da zama a jam’iyar ta NNPP.

Ta ƙara da cewa matakin da ta ɗauka na da alaƙa kan yadda aka ƙi bawa mutanenta  muƙami a gwamnatin Kano tun bayan da aka kafa gwamnatin.

Ta kuma bayyana biyayya ta ga jagoran jam’iyar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

A ƴan kwanakin nan dai ƴaƴan jam’iyar ta NNPP na cigaba da nuna rashin jin daɗinsu kan yadda aka yi watsi da su tun bayan kafa gwamnati.

More from this stream

Recomended