Gwamnatin jihar Kano ta sanar da rage awanni aiki ga ma’aikatan a jihar a cikin watan azumin Ramadan.
Sanarwar rage awannin aikin na kunshe ne cikin wata sanarwa da ofishin shugaban ma’aikatan jihar ya fitar a ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce daga mako mai zuwa za a riƙa buɗe ofisoshin gwamnati da ƙarfe 08:00 na safe a kuma rufe su da ƙarfe 03:00 na rana daga ranar Litinin zuwa Alhamis a yayin da lokacin zuwa aiki ranar Juma’a yana nan a yadda yake.
A ƙarshe sanarwar ta yi kira ga ma’aikatan da suyi amfani da lokacin wajen bautawa ubangijinsu tare addu’ar samun zaman lafiya