Gwamnatin Kano ta rage awannin lokacin aiki a watan Ramadan

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da rage awanni aiki ga ma’aikatan a jihar a cikin watan azumin Ramadan.

Sanarwar rage awannin aikin na kunshe ne cikin wata sanarwa da ofishin shugaban ma’aikatan jihar ya fitar a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce daga mako mai zuwa za a riƙa buɗe ofisoshin gwamnati da ƙarfe 08:00 na safe  a kuma rufe su da  ƙarfe 03:00 na rana  daga ranar Litinin zuwa Alhamis a yayin da lokacin zuwa aiki ranar Juma’a yana nan a yadda yake.

A ƙarshe sanarwar ta yi kira ga ma’aikatan da suyi amfani da lokacin wajen bautawa ubangijinsu tare addu’ar samun zaman lafiya

More from this stream

Recomended