Rahotanni da ke fitowa daga fadar shugaban kasa na nuna cewa Shugaba Tinubu ya dakatar da ministar ji kai saboda zargin badakalar kudi.
An bayyana dakatarwar ne a wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaba Tinubu, Ajuri Ngelale, ya rattaba wa hannu a yau Litini.
Wannan dakatarwa tana da alaƙa da wasu zarge-zarge da ministar ke fuskanta na ƙoƙarin karkatar da wasu maƙudan kuɗaɗe ta ɓarauniyar hanya.