Allah Ya yi rasuwa wa Sheikh Abubakar Giro Argungu

Babban malamin Musulunci a Najeriya Sheik Abubakar Giro Argungu ya riga mu gidan gaskiya.

Sanarwar mutuwar tasa ta fito ne a yau Laraba ya shafinsa na Facebook wanda ake kyautata zaton a hannun ɗalibansa yake.

Sanarwar ta ce:

“INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN!

“Allah Yayiwa Sheikh Giro Argungu Rasuwa, Bayan Jinya Da Ya Samu A Daren Jiya, Bayan Kammala Tafsir Magriba Zuwa Ishaa, Allah Yayi Maka Gafara Sheikh Amin..

“Wednesday!
6th September, 2023.”

Muna addu’ar Allah Ubangiji Ya gafarta masa, Ya sa Aljanna ce makomarsa.

More from this stream

Recomended