Mutanen da basu gaza 19 ne ba suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru akan titin Damaturu zuwa Potiskum a ranar Alhamis.
A cewar sakataren asibitin Damagum, Mallam Hamisu Muazu hatsarin ya faru a wajen garin Fune dake karamar hukumar Fune ta jihar.
Ya ce hatsarin ya rutsa da motoci uku kirar Golf da suka yi tawo mu gama inda biyu daga ciki na dauke da fasinjoji da za su je biki jihar Borno.
A cewar sa mutane 19 ne suka mutu nan take kuma 12 daga ciki sun fito ne daga zuriya guda.
Ya kara da cewa yara biyu ne suka tsira daga hatsarin.