10.3 C
London
Thursday, November 7, 2024
HomeMoreIyaye biyu na ɗaliban Islamiyyar da aka sace a Neja sun rasu

Iyaye biyu na ɗaliban Islamiyyar da aka sace a Neja sun rasu

Date:

Related stories

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...
spot_imgspot_img
mace na kuka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Sace yara a makarantu a Najeriya na neman zama ruwan dare, al’amarin da ke jefa iyaye cikin tasku

Iyaye mata biyu na ɗaliban makarantar Islamiyyar garin Tegina sun rasu sakamakon kaduwar da suka yi bayan da suka sami labaran sace ‘ya’yansu da ‘yan bindiga suka yi, a cewar Hukumar makarantar.

Shugaban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko Islamiyya ta ƙaramar hukumar Rafi a jihar Neja, Malam Abubakar Garba Alhassan ne ya shaida wa BBC hakan a wata hira a ranar Laraba.

Ya ce iyayen sun rasu ne bayan da ‘yan bindigar suka kira shugaban makarantar ta waya inda suka bukaci a biya miliyoyin kudin fansa ko kuma su kashe ɗaliban.

Malam Abubakar Garba Alhassan shugaban makarantar Islamiyyar ya ce daga ranar Talata zuwa ranar Laraba ‘yan bindigar sun kira shi kusan sau goma.

“Sun ce min idan har ba mu tura waɗannan kuɗaɗe da suka nema ba to ba asararsu ba ce su kashe waɗannan yaran.

Ɗaya daga cikin iyayen da suka rasun a wani ƙauye take, “dama ta turo ɗanta ne garin Tegina yake zaune da ƙanwarta don zuwa makarantar.

“To da aka kai mata labari tun ranar sai ta faɗi ta suma aka kai ta asibiti, kafin wani ɗan lokaci ta cika.

“Ita kuwa ɗayar yau (Laraba) ne ta rasu, ɗazun nan na dawo daga jana’izarta da rana. Ita ma tun ranar da ta ji labarin ba ta da lafiya yau kuwa Allah Ya karɓi abarsa,” in ji hedimasta.

Tagayyara

Malam Abubakar ya ce ya samun yin magana da malamai uku na makarantar da ƴan bindigar suka sace tare da yaran, kuma ɗaya daga cikinsu ta bayyana masa irin halin ƙunci da uƙubar da suke ciki.

“Ta ce min a jiya (Talata) an bubbuge su sannan ƙananan yaran da ba su wuce shekaru huɗu zuwa biyar ba ba sa ko iya tafiya.

“Sannan an ciccire musu riguna daga su sai wandon makaranta ko takalma babu a ƙafafunsu babu kuma hijabi atare da su.

“Wasun su ma na zaune ne a rana a ƙasa ba a cikin inuwa ba,” kamar yadda ya bayyana cikin damuwa.

Shugaban makarantar ya ce mafi akasarin yaran mata ne kuma ƙanana.

Ya ce a yanzu haka yana cikin tashin hankali musamman kan barzanar da ƴan bindigar suka yi cewa za su kashe yaran.

Cikin kuka malamin ya ce: ‘Yanzu haka duk wani baƙin cikin duniya ya dabaibaye ni a matsayina na hedimastan wannan makarantar. Na rantse da girman allah ba zan iya bayyana maka halin baƙin cikin da nake ciki ba.

Sai dai ya ce gwamnati ta san halin duk da ake ciki na barazanar ƴan bindigar, kuma iyayen yaran sun so yin zanga-zanga amma suka lallashe su suka hana su.

Gwamnatin dai ba ta shaida musu wata magana sahihiya ba kan batun kuɗin fansar da ƴan bindigar suka sace in ji shi.

“Muna magana da shugaban ƙaramar hukuma wanda ke ba mu haɗin kai sosai tare da taimaka wa iyayen yara. Kuma jiya na yi magana da sakataren gwamnati ta hanyar matarsa kuma ya yi alƙwarain yin wani abu akai.

“Amma ka san lamarin gwamnati ba lallai ya kasance yanzu-yanzu ba,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

Wasu labaran da za ku so

Ruwan dare

Tuni dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba jami’an tsaro umarnin gaggauta ceto ɗaliban Islmiyyar da aka sace a jihar Neja.

Yanzu satar daliban makaranta a Najeriya ya zama ruwan dare, kuma yanzu satar ɗaliban ta koma har ɗaliban makarantun gaba da sakandare.

Ko a watan Fabirairu sai da aka sace ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma’aikata guda 41 a Jihar.

A makon da ya gabata ne aka saki ɗaliban Jami’ar Greenfield a jihar Kaduna bayan kashe wasu daga cikinsu. Wannan na zuwa bayan sako ɗaliban Kwalejin gandun daji da ke Kaduna.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here