Iyaye biyu na É—aliban Islamiyyar da aka sace a Neja sun rasu

mace na kuka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Sace yara a makarantu a Najeriya na neman zama ruwan dare, al’amarin da ke jefa iyaye cikin tasku

Iyaye mata biyu na É—aliban makarantar Islamiyyar garin Tegina sun rasu sakamakon kaduwar da suka yi bayan da suka sami labaran sace ‘ya’yansu da ‘yan bindiga suka yi, a cewar Hukumar makarantar.

Shugaban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko Islamiyya ta ƙaramar hukumar Rafi a jihar Neja, Malam Abubakar Garba Alhassan ne ya shaida wa BBC hakan a wata hira a ranar Laraba.

Ya ce iyayen sun rasu ne bayan da ‘yan bindigar suka kira shugaban makarantar ta waya inda suka bukaci a biya miliyoyin kudin fansa ko kuma su kashe É—aliban.

Malam Abubakar Garba Alhassan shugaban makarantar Islamiyyar ya ce daga ranar Talata zuwa ranar Laraba ‘yan bindigar sun kira shi kusan sau goma.

“Sun ce min idan har ba mu tura waÉ—annan kuÉ—aÉ—e da suka nema ba to ba asararsu ba ce su kashe waÉ—annan yaran.

ĆŠaya daga cikin iyayen da suka rasun a wani Ć™auye take, “dama ta turo É—anta ne garin Tegina yake zaune da Ć™anwarta don zuwa makarantar.

“To da aka kai mata labari tun ranar sai ta faÉ—i ta suma aka kai ta asibiti, kafin wani É—an lokaci ta cika.

“Ita kuwa É—ayar yau (Laraba) ne ta rasu, É—azun nan na dawo daga jana’izarta da rana. Ita ma tun ranar da ta ji labarin ba ta da lafiya yau kuwa Allah Ya karÉ“i abarsa,” in ji hedimasta.

Tagayyara

Malam Abubakar ya ce ya samun yin magana da malamai uku na makarantar da ƴan bindigar suka sace tare da yaran, kuma ɗaya daga cikinsu ta bayyana masa irin halin ƙunci da uƙubar da suke ciki.

“Ta ce min a jiya (Talata) an bubbuge su sannan Ć™ananan yaran da ba su wuce shekaru huÉ—u zuwa biyar ba ba sa ko iya tafiya.

“Sannan an ciccire musu riguna daga su sai wandon makaranta ko takalma babu a Ć™afafunsu babu kuma hijabi atare da su.

“Wasun su ma na zaune ne a rana a Ć™asa ba a cikin inuwa ba,” kamar yadda ya bayyana cikin damuwa.

Shugaban makarantar ya ce mafi akasarin yaran mata ne kuma ƙanana.

Ya ce a yanzu haka yana cikin tashin hankali musamman kan barzanar da Ć´an bindigar suka yi cewa za su kashe yaran.

Cikin kuka malamin ya ce: ‘Yanzu haka duk wani baĆ™in cikin duniya ya dabaibaye ni a matsayina na hedimastan wannan makarantar. Na rantse da girman allah ba zan iya bayyana maka halin baĆ™in cikin da nake ciki ba.

Sai dai ya ce gwamnati ta san halin duk da ake ciki na barazanar Ć´an bindigar, kuma iyayen yaran sun so yin zanga-zanga amma suka lallashe su suka hana su.

Gwamnatin dai ba ta shaida musu wata magana sahihiya ba kan batun kuÉ—in fansar da Ć´an bindigar suka sace in ji shi.

“Muna magana da shugaban Ć™aramar hukuma wanda ke ba mu haÉ—in kai sosai tare da taimaka wa iyayen yara. Kuma jiya na yi magana da sakataren gwamnati ta hanyar matarsa kuma ya yi alĆ™warain yin wani abu akai.

“Amma ka san lamarin gwamnati ba lallai ya kasance yanzu-yanzu ba,” kamar yadda ya Ć™ara da cewa.

Wasu labaran da za ku so

Ruwan dare

Tuni dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba jami’an tsaro umarnin gaggauta ceto É—aliban Islmiyyar da aka sace a jihar Neja.

Yanzu satar daliban makaranta a Najeriya ya zama ruwan dare, kuma yanzu satar É—aliban ta koma har É—aliban makarantun gaba da sakandare.

Ko a watan Fabirairu sai da aka sace É—aliban makarantar Kagara da malamansu da ma’aikata guda 41 a Jihar.

A makon da ya gabata ne aka saki É—aliban Jami’ar Greenfield a jihar Kaduna bayan kashe wasu daga cikinsu. Wannan na zuwa bayan sako É—aliban Kwalejin gandun daji da ke Kaduna.

More News

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ĆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...

Musulmi a Zaria sun yi taron addu’o’i saboda mummunan halin matsi da Najeriya ke ciki

Musulmi a garin Zaria na jihar Kaduna, sun gudanar da addu'a ta musamman domin neman taimakon Allah kan halin da 'yan Najeriya ke ciki...