Ƴan Boko Haram Sun Yiwa Manoma 10 Yankan Rago

Wasu da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne sun yanka akalla manoma 10 a garin Kawuri dake karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.

A cewar mazauna garin da kuma majiyoyin jami’an tsaro lamarin ya faru a ranar Litinin da misalin karfe 08:15 na safe.

Wannan harin na zuwa ne yan makonni kadan bayan da yan ta’addar suka kashe akalla manoma 15 a kananan hukumomin Damboa da Jere.

A cewar Mallam Mohammed Sheriff dake garin yan ta’addar sun bi sahun manoman inda suka kashe su a gonakinsu dake kusa da madatsar ruwa ta Alau.

“Manoman suna aiki a gonakinsu lokacin da maharan suka far musu suka yi musu yankan rago yanzu muna yiwa gawarwakin sutura domin binnewa.”A cewar Sheriff.

More from this stream

Recomended