Ƴan bindiga sun kashe ɗan sanda da wasu mutane uku a Abia

Ƴan bindiga sun kashe Shehu Oyibo wani insifectan ƴan sanda da wasu mutane uku a jihar Abia.

An yi kisan ne a ranar Lahadi akan titin Ngwa dake garin Aba  yayin wata musayar wuta tsakanin maharan da kuma jami’an ƴan sandan da suke gudanar da sintiri.

Maureen Chinaka, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Abia ta ce biyu daga cikin ƴan bindigar sun mutu a yayin musayar wuta.

Chika Godliveth, Onyenaturuchi Jonah, a Eniobong Godsgift Clement su ne sauran mutanen da aka kashe a harin.

Chinaka ta ce an ajiye gawar mutanen a ɗakin ajiye gawarwaki.

Ta tabbatarwa da al’umma cewa rundunar za ta cigaba da tsaron rayukansu kuma tuni aka fara gudanar da bincike kan harin.

Jihar ta Abia na ɗaya daga cikin jihohin yankin kudu maso gabas da suke fuskantar matsalolin tsaro sakamakon ayyukan mayaƙan ƙungiyar IPOB dake fafutukar neman kafa ƙasar Biafara.

More from this stream

Recomended