Zulum ya jagoranci raba kayan abinci a Gwoza

A karshen makon da ya kai ziyarar jin kai da ci gaba a garin Gwoza na jihar Borno, Gwamna Babagana Umara Zulum a ranar Lahadin da ta gabata ya sa ido kan rabon kayan abinci ga gidaje sama da 13,000 wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.

An gudanar da rabon kayayyakin ne a harabar fadar Sarkin Gwoza, Shehu Idrissa Timta.

Zulum wanda ya je Gwoza a ranar Asabar, ya kai ziyarar ba-zata zuwa babban asibitin da tsakar dare inda ya ba da umarnin a kai wa asibitin dauki cikin gaggawa.

Zulum, tare da sabon Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Barkindo Mohammed Saidu ne suka jagoranci rabon kayayyakin, domin tabbatar da an kai wa dukkan iyalai da suka cancanta.

More from this stream

Recomended