Zababbun hotunan karshen mako na Afirka | BBC Hausa

An zabo wasu daga cikin hotunan abubuwan da suka faru a nahiyar Afirka da kewaye:

Zaki ya bude bakinsa a lokacin da ya ke cikin kejin da aka rufe shi.

Hakkin mallakar hoto
Barcroft Media

Image caption

Wannan zakin na daya daga cikin zakuna biyar da aka dauke daga wani gidan adana namun daji da ke Ukraine inda aka kai su wata cibiyar gyara halinka da ke kasar Afirka ta Kudu a ranar Litinin din da ta gabata.

Wata da namiji na rawar ballet a kan wani dandamali a Kenya.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Dalibai masu rawar Ballet na rawa a wani dakin taro a Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

Wani mutum na wuce wa ta jikin wani farin dutse da ke kudancin kasar Masar a ranar Asabar.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wani lebura yana wuce wa ta kusa da wani bango a mahakar ma’adanin siminti da ke Farin Tsauni a kudancin kasar Masar.

Ruth Akulu da kawayenta a lokacin da suke yanka kek domin murnar kammala karatunsu na jami'a.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wasu dalibai da suka kammala karatun jami’a a yayin da suke yanka kek domin murnar kammala karatunsu a ranar Asabar a Kampala, babban birnin kasar Uganda.

Wani mutum na fentin zanen da ya yi.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A ranar Jumma’a, wani mai zane a Eritiriya Nebay Abraha, ya zana wani zane a wajen aikinsa da ke Addis Ababa babban birnin kasar Habasha.

Mutane tsaye a barandar gidajensu suna kallon abubuwan da ke faruwa a waje.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wasu mutane a Nairobi na kallon baraguzan wani gini mai hawa shida da ya rushe a safiyar ranar Jumma’a inda mutum 10 suka rasa ransu.

Inuwar wata mata ke nan da ake gani ta wata taga da ruwan sama fallatsawa inda ta ke wucewa.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

A ranar Litinin, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya sanya wata taga yin dishi-dishi a Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.

Sarauniyar kyau mai barin gado 'yar Philippines na sanya kambun lashe gasar ta bana a kan Zozibini Tunzi, 'yar Afirka ta Kudu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Zozibini Tunzi, ‘yar kasar Afirka ta Kudu da ta lashe gasar sarauniyar kyau ta duniya a Amurka, inda ta ce ta tashi a cikin wata rayuwa wadda ake kallon mace kamar ta ba ta da kyau.

Mutane a wani daji na kallon mutum-mutumin wani katon tsuntsu da aka ajiye.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wani katon shaho da wani mai zane dan kasar Senegal Soly Cisse ya sassaka wanda aka a jiye shi a wani gidan adana namun daji da ke Abidjan, na kasar Ivory Coast.

Masu wasa da dawakai na sukuwa a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A ranar Alhamis, wasu masu wasa da dawakai suka kai gaisuwarsu ga shugaban kasar Habasha, Abiy Ahmed, bayan da ya samu kyautar lambar yabo ta Nobel.

Faduwar rana a tsibirin Praslin da ke Seychelles a ranar Jumma'a.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Faduwar rana a tsibirin Praslin da ke Seychelles a ranar Jumma’a.

An zabo hotunan ne daga Getty da EPA da Barcroft Media da AFP da kuma Reuters.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...