Za a yi wa NYSC garambawul

Gwamnatin tarayya ta ce za ta fara yin nazari, gyara da kuma yin garambawul ga hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) domin biyan bukatun nan gaba.

Ministar ci gaban matasa, Dakta Jamila Ibrahim, ne ta bayyana haka a wajen bude taron. 

Babban taron masu yi wa kasa hidima na NYSC ya gudana ne tare da shugabannin manyan makarantu a Najeriya, wanda aka gudanar a Cibiyar Shari’a ta kasa da ke Abuja, a ranar Litinin.

Ministar ta kuma bayyana cewa sama da mambobin kungiyar 5000 za a ba su ayyukan na kasuwanci da har zai kai naira miliyan 10.

More from this stream

Recomended