Za a sake wasan Shrewsbury da Liverpool a Anfield

FA Cup

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kungiyar Liverpool ta tashi 2-2 da Shrewsbury a wasan zagaye na hudu a gasar FA Cup da suka fafata ranar Lahadi.

Liverpool wadda rabon ta kai zagaye na biyar a FA Cup tun 2015 ta fara cin kwallo ne ta hannun Curtis Jones daga baya Donald Love ya ci gida.

Shrewsbury mai buga League One ta farke kwallayenta cikin minti 10 a damar makin da ta samu ta hannun Jason Cummings.

Tun farko magoya bayan Shrewsbury sun yi kuwa a lokacin da aka cire Callum Lang, sannan Cummings ya canje shi.

Cummings din ya ci kwallon farko a bugun fenariti, sannan ya farke ta biyu da hakan ya sa sai dai a buga wasa na biyu nan gaba a Anfield.

Tun kan tashi daga karawar Jurgen Klopp ya saka Mohamed Salah da Roberto Firmino don kada wankin hula ya kai su dare.

Ranar Litinin za a raba jadawalin zagaye na biyu, sannan a tsayar da ranar da Shrewsbury za ta ziyarci Anfield a karawa ta biyu.

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...