Za a kaddamar da majalisar dokoki karo na 9 a Najeriya

Majalisar dokokin Najeriya

—BBC Hausa

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A yau ne ake kaddamar da majalisar dokokin Najeriya wadda ta kunshi bangaren dattawa da wakilai.

Ana kuma sa ran zaben shugabannin majalisar.

Da dama daga cikin ‘yan majalisar dattawan da ‘yan majalisar wakilan sabbi ne, ko da yake akwai wadanda suka dade.

Majalisar dokokin Najeriya dai ita ce zuciyar dimokradiyya mafi girma a nahiyar Afirka don haka ne irin mutanen da ke cikinta ke gagarumin tasiri ko mai kyau ko marar kyau wajen tafiyar da kasa.

Wannan ne dai karo na tara da ake kaddamar da majalisar dokoki a kasar wadda ta hada majalisar dattawa mai kujeru 109 da kuma ta wakilai mai kujeru 360.

A kowanne lokaci a majalisar, shugabancin bangarori biyu na majalisar na da tasiri kwarai da gaske kan yadda dangantaka zata kasance da bangaren zartaswa.

Duka majalisun biyu na tarayyar Najeriya dai sun sha fuskantar kalubale da dambarwa iri-iri kama daga bai wa hammata iska yayin zama zuwa ga tsige shugabanni galibi saboda muradu na siyasa.

Ana dai yawan samun matsaloli ko rashin fahimta a tsakanin ‘yan majalisar abin da a wani lokaci kan jawo tsaiko ko jan kafa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyan ‘yan majalisar.

A ranar Talata 11 ga watan Yuni ne sababbin ‘yan Majalisar Tarayya a Najeriyar za su sha rantsuwar kama aiki.

‘Yan majalisar za su maye gurbin wadanda suka gabatar da aiki ne daga shekarar 2015 zuwa 2019, kuma ita ce majalisa ta tara.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...