Za a hukunta Ibrahimovic kan mallakar kamfanin caca

Zlatan Ibrahimovic

Hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA za ta binciki Zlatan Ibrahimovic kan zargin hada hannun mallakar wani kamfanin caca.

Wasu rahotanni daga Sweden na cewar dan kwallon AC Milan, mai shekara 30 ya karya ka’idar hukumar, bayan da ya yi hadakar mallakar kamfanin caca.

Dokar hukumar kwallon kafar Turai ta fayyace cewar kada dan wasa ya saka jari ko hannu a kamfanin caca.

A makon jiya ne Ibrahimovic ya tsawaita kwantiragin ci gaba da taka leda a AC Milan, bayan da ya cika shekara 40 da haihuwa.

Tsohon dan wasan Manchester United ya ci kwallo 17 a wasa 25 a dukkan fafatawar da ya yi a kakar bana.

Ibrahimovic ya koma buga wa tawagar kwallon kafa ta Sweden tamaula, bayan shekara biyar da yin ritaya.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...