Za a fara shari’ar jagoran harin 11 ga Satumba a Amurka | BBC Hausa

Khalid Sheikh Mohammad

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An kama Khalid Sheikh Mohammad a Pakistan a shekara ta 2003

An tsayar da ranar fara shari’a ga mutane biyar da suka hada da Khalid Shaikh Mohammed, wanda ake zargi da shi ne kanwa-uwar-gami wajen shirya harin ranar Talata 11 ga watan Satumba da aka kai Amurka a 2001.

Wani alkali soji ya ce za a fara zabar masu taimaka wa alkali yanke hukunci a ranar 11 ga watan Janairu na shekara ta 2021, a sansanin Guantanamo Bay da ke Cuba.

Ana tuhumar mutanen ne da laifukan da suka hada da ta’addanci da kuma kisan kai na kusan mutane dubu uku, kuma idan har aka same su da laifi, za a yanke musu hukuncin kisa.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Lokacin da aka gurfanar da Motassadek a wata kotu a Jamus a 2005

Amurka ce dai ta kama Khalid Shaikh Mohammed, a Pakistan, a shekara ta 2003, mutumin da take zargi da shi ne kanwa uwar gamin harin na 11 ga watan Satumba, na 2000.

Shekara uku bayan damke shi ne, sai ta aika da shi sansaninta na kare kukanka na Guantanamo Bay da ke Cuba.

Da farko dai an fara tuhumarsa, shi da mukarrabansa da ake zargin sun hada baki wajen kai harin a lokacin mulkin George W. Bush, amma kuma sai aka jinkirta shariar, lokacin da Shugaba Obama ya yi kokarin mayar da shariar zuwa wata kotun farar hula a birnin New York.

To amma kuma sai aka yi watsi da shirin hakan bayan da matakin ya jawo surutu daga jama’a.

Shi dai Obama ya kafa gwamnati a shekara 2009, inda ya yi alkawarin rufe sansanin na Guantanamo Bay ya kuma yi wa jiga-jigan wadanda Amurka ke zargi da laifukan ta’addanci a kotunan farar hula na Amurka.

Amma wannan ce-ce-ku-ce da hakan ya jawo ya sa ya yi watsi da shirin rufe sansanin ma, saboda batun inda za a tsare, tare da yi wa wadanda ake zargi da kasancewa ‘yan kungiyar al-Qaeda shari’a ya zama abu mai wuyar gaske.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Zanen hoton Khalid Sheikh Mohammed, wanda Amurka ke zargi da kitsa harin na 9/11

A shari’ar dai ana tuhumar Khalid Shaikh Mohammed, a matsayin wanda ya kitsa harin da ya yi sanadiyyar hallaka mutane 2,976.

Mutane goma sha tara ne suka yi fashin jiragen fasinja hudu, inda suka kara biyu daga ciki a dogon ginin Cibiyar Kasuwanci ta Duniya a New York, daya a ma’aikatar tsaro da Amurka, Pentagon a Washington, na hudun kuwa suka fada da shi wani fili a Pennsylvania.

Wannan ne karon farko da aka tsayar da ranar fara shariar, kuma idan har komai ya tafi yadda aka tsara, za a fara shariar kenan wata takwas daidai kafin cika shekara 20 da kai harin na 11 ga watan Satumba.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...