Za a ci gaba da wasannin neman shiga Gasar kofin Afirka

0
Afcon Qualifiers

Ranar Laraba za a ci gaba da wasannin neman gurbin shiga gasar Cin Kofin nahiyar Afirka da za a fafata a 2021.

Kimanin wasa 48 za a kara, inda tawagogin kasashen za su ci gaba da buga wasanni na uku- uku, wasu kuma na hur-hudu a cikin rukuni.

Wasu kasashen ma sun dauki sabbin masu horar da tamaula da suke sa ran za su kai su gasar da za a yi a Kamaru.

Tun farko bullar cutar korona ce ta dagula komai da tasa dole aka dakatar da wasannin aka kuma dage gasar kamar yadda aka tsara tun farko da za a yi cikin 2021.

Saura wasanni hur-hudu da suka rage don samun kasashe 24 da za su wakilci Afirka a gasar da za a buga, wacce za a yi a 2022.

Kawo yanzu ‘yan wasa uku ne ke kan gaba wajen cin kwallo a wasannin da suka hada da Victor Osimhen na Najeriya.

Sauran sun hada da Famara Diedhiou na Senegal da kuma Wahbi Khazrina Tunisia.

Algeria ce mai rike da kofi, wacce ta zama zakara a gasar da aka yi a Masar a 2019.

Wasannin da za a buga ranar Laraba 11 ga watan Nuwamba 2020:

 • Uganda da Sudan ta Kudu
 • Senegal da Guinea-Bissau
 • Kenya da Tsibirin Comoros
 • Mauritania da Burundi
 • Cape Verde da Rwanda
 • Libya da Equatorial Guinea

Ranar Alhamis 12 ga watan Nuwamba 2020:

 • Kamaru da Mozambique
 • Zambiada Botswana
 • Ghana da Sudan
 • Algeria da Zimbabwe
 • Ivory Coast da Madagascar
 • Burkina Faso da Malawi
 • Gabon da Gambia

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here