Sanatocin da aka zaɓa daga yankin arewa sun dage cewa dole sai shugaban majalisar dattawa ya fito daga yankin arewacin kasarnan.
Wasu bayanai sun bayyana cewa zaɓaɓbun sanatocin 39 cikin 58 da suka fito daga jam’iyyu daban-daban sun gudanar da wani taro ranar Lahadi a Abuja inda suka cimma matsaya kan batun.
Wani sanata daga shiyar arewa maso yamma da yafi so kada a bayyana sunansa ya ce sanatoci da suka fito daga arewa sun dage sai shugaban majalisar dattawa ya fito daga yankin domin sakawa yankin kan goyon bayan takarar Bola Ahmad Tinubu a zaɓen da wuce.
Ya ce taron ya yanke matsayar tuntubar takwarorinsu da suka fito daga yankin kudu domin samun goyon bayansu.
