Yemen: Gomman Ć´an ci-rani sun halaka bayan da kwale-kalensu ya nutse a teku

File photo showing a boat carrying migrants in Aden, Yemen, before they are deported to Somalia (26 September 2016)

Asalin hoton, AFP

Ana fargabar gomman ƴan ci-rani ƴan Afirka sun halaka bayan da kwale-kalensu da ke ɗauke da su ya nutse a kusa da gaɓar tekun Yemen.

Masunta a lardin Lahj na ƙasr ta Yemen sun sanar da kamfanin dillancin labarai na AFP cewa sun tsamo gawarwaki 25 daga teku kusa da Ras-al-Ara.

Wani jami’in gwamnati a yankin ya ce wani kwale-kwale dauke damutum 160 zuwa 200 ya nutse a yankin kwanaki biyu da su ka gabata.

Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da Yan Gudun Hijira (IOM) ya ce yana ƙoƙarin tabbatar da sahihancin rahotannin da ke cewa wani kwale-kwale ɗauke da gomman ƴan ci-rani ya nutse.

Wata jaridar intanet ta ƙasar Yemen mai suna Aden al-Ghad ta ruwaito wasu ganau na cewa ƴan ci-ranin da su ka halaka za su kai 150, kuma akwai ƴan Yemen huɗu a cikin waɗanda kawo yanzu sun ɓace tare da wasu ƴan ci-ranin.

Bayanan hoto,
Taswira na nuna Yemen da Djibouti da kuma Ras al-Ara

Ras al-Ara wani yanki ne da ke gaɓar teku da masu fasa-ƙwaurin mutane ke amfani da shi, wanda ke gabas da mashigar ruwa ta Bab al-Mandab mai faɗin kilomita 20 wadda ta raba Yemen da Djibouti kuma ta haɗa tekun Bahar al-Ahmar da yankin tekun Gulf na Aden.

A Ć´an shekarun nan, É—aruruwan dubban Ć´an ci-rani daga Afirka – yawancinsu Ć´an Habasha da Somaliya – sun tsallaka teku a wannan wurin zuwa Yemen a wani yunĆ™uri na isa Saudiyya.

Bayanan bidiyo,
Yadda Ć´an ci-rani ke kwarara Saudiyya a hanya mai cike da hatsari

Kana yawancin kwale-kwalen da masu fasa-ƙwaurin mutanen ke amfani da su ba su da inganci, baya ga maƙare su da su ke yi da mutane, yanayin da ke haifar da hatsarurruka.

A watan Afrilu, a ƙalla ƴan ci-rani 44 sun rasa rayukansu bayan da wani kwale-kwale mallakar masu fasa-ƙwaurin mutane ya nutse a kan hanyarsa ta zuwa Yemen daga Djibouti.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...