‘Yara ‘yan gudun hijira sama da dubu 800 ba su zuwa makaranta’ – MDD

EPA

Hakkin mallakar hoto
EPA

Hukumar majalisar dinkin duniya mai kula da ‘yan gudun hijira ta fitar da wani rahoto inda ta bayyana cewa cikin yara ‘yan gudun hijira miliyan daya da dubu dari bakwai na duniya, rabinsu ba su samun ilimin boko.

Ta bayar da dalilai da suka hada da bukatar bayar da muhimmanci ga kare lafiyar yara sama da ba su ilimi, da kuma gazawar da iyayen yara ke yi na kasa biyan kudin makaranta.

Hukumar ta ce damar da yara ‘yan gudun hijira ke da ita na samun ilimin sakandare na dada raguwa yayin da suke kara girma.

Hukumar ta yi kira ga gwamnatoci da kuma makarantu da kamfanoni masu zaman kansu da zuba jari wajen fito da kyakyawan shiri da zai tabbatar yaran sun samu rayuwa mai inganci.

Ko a kwanakin baya sai da Majalisar wakilai a Amurka ta amince da wani kudurin doka inda za a samar da dala miliyan hudu da dubu dari shida domin tallafawa masu fama da matsi da kuma fatara da ke kan iyakar kasar.

Shi ma Fafaroma Francis a kwanakin baya ya bayar da tallafin dalar Amurka dubu 500 ga ‘yan gudun hijira.

Dama hukumar hukumar amjalisar dinkin duniya mai kula da ‘yan gudun hijirar ta bayyana cewa yawan mutanen da tashin hankali ya raba da muhallansu ya wuce miliyan 70, adadi mafi girma da aka taba gani a tarihi.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...