Mambobin kungiyar yan uwa musulmi ta Najeriya da aka fi sani da Shi’a sun kona tutocin kasar Amurka da Isra’ila yayin wata gagarumar zanga-zanga da suka gudanar a birnin tarayya Abuja.
Masu zanga-zangar da suka taru a mahadar titin kasuwar Wuse sun bayyana kasashen biyu a matsayin makiya dake musguna wa kasar FalasÉ—inu.
Abdullahi Musa mai magana da yawun kungiyar ya ce an kona tutocin ne domin nuna fushinsu kan halayyar kasashen biyu.
An nuna tutocin biyu ga dandazon taron jama’a dake dauke da butuntumin Donald Trump shugaban kasar Amurka kafin a watsa musu fetur a cinna wuta.
Kungiyar ta ce an gudanar da zanga-zangar ne domin sanar da bukatarsu ta neman a saki jagoransu Sheikh Ibrahim Elzakzaky domin yaje likitoci su duba lafiyarsa.