Yan shi’a 1000 sun bace a zanga-zangar Abuja

Ƙungiyar Yan Uwa Musulmi ta Najeriya wato shi’a ta bayyana cewa mambobin kungiyar 1000 ne suka bace bayan artabun da suka yi da jami’an tsaro a birnin tarayya Abuja.

Mambobin sun shafe kwanaki uku suna zanga-zanga a birnin tarayya Abuja duk da cewa sojoji da Æ´ansanda sun gargade su kan yin haka.

A yayin zanga-zangar ne aka kashe wasu daga cikinsu wasu da dama suka samu raunuka ya yin da aka kama mutane 400.

A wata sanarwa ranar Laraba, Abdullahi Musa mai magana da yawun kungiyar ya ce kari kan mutane 1000 da suka bace an kashe 46 ya yin da mutane 107 suka jikkata.

Ƙungiyar ta ci alwashin cigaba da zanga-zangar neman a saki shugaban su, Sheikh Ibrahim Elzakzaky ba tare da gindaya wasu sharuda ba.

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...