‘Yan Real Madrid da za su kara da Chelsea a Ingila | BBC Hausa

Real Madrid

Asalin hoton, Real Madrid

Real Madrid ta je Stamford Bridge domin buga wasa na biyu na daf da karshe a Champions League da za su fafata ranar Laraba.

A makon jiya ranar Talata kungiyoyin suka tashi 1-1 a Spaniya a wasan farko na daf da karshe a gasar ta Zakarun Turai.

Tuni kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana ‘yan wasan da za su fuskanci Chelsea a wasa na biyu a Stamford Bridge.

Duk wadda ta yi nasara za ta buga wasa ne da Manchester City wadda ta kai karawar karshe a karon farko a Champions League, bayan da ta doke PSG da ci 4-1 gida da waje.

‘Yan wasan Real Madrid da suka je Ingila:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: E. Militao da Sergio Ramos da Nacho da Marcelo da Odriozola da Mendy da kuma Miguel.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modric da Casemiro da Isco da Valverde da Arribas da kuma Blanco.

Masu cin kwallaye: Hazard da Benzema da Asensio da Vini Jr. da Mariano da kuma Rodrygo.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...