
Wasu da ake zargin yan fashin daji ne sun yi garkuwa da manoma hudu a kauyen Tudun Moriki dake karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi lamarin ya faru ne da tsakar ranar Alhamis lokacin da manoman suke aiki a gonakinsu.
Makama ya ce yan fashin daji dauke da makamai sun farma gonakin manoman da misalin karfe 12:00 na rana inda suka dauke su da karfin tsiya ya zuwa wani wurin da baa sani ba.
Jami’an tsaro sun garzaya ya zuwa wurin a matsayin martani kan sace mutanen.
Makama ya kara da cewa tuni jami’an tsaron suka gaggauta kaddamar da aikin ceto manoman inda ya ce ana cigaba da bin diddigin yan bindigar domin kubutar da manoman lafiya.