‘Yan Fashi Sun Fara Addabar Birnin Yamai Da Tsakar Rana

VOA Hausa

Mazaunan Yamai babban birnin jamhuriyar Nijar sun fara nuna damuwa game da yanayin tabarbarewar tsaron da aka shiga a ‘yan kwanakin nan inda ‘yan fashi da makami ke afkawa mutane da rana tsaka akan hanyar bankuna ko kuma cikin unguwanni.

A shekarun baya birnin Yamai na daga cikin manyan biranen da ake sakawa a jerin wadanda ke da cikakken tsaro a yankin Afrika ta yamma.

Sai dai da alama abubuwa sun fara canzawa idan aka yi la’akkari da yadda barayi suka fara tare titi suna afkawa wadanan suka ciri kudi a banki ko wadanda ke shirin kai ajiya.

Irin haka ta faru ga wasu ‘yan kasar waje a karshen makon jiya bayan sun dauko kudi daga banki, ko da yake rana ta baci wa wadanan barayi har ma aka kama 1 daga cikinsu.

Wani magidanci Laouali Boubacar ya nuna damuwa a game da yadda sha’anin tsaro ke tabarbarewa a halin yanzu.

Wani rukuni na 2 na ‘yan fashi dauke da bindiga ya afkawa motar wani shagon sayar da kayan abinci da ake kira ETS HOUDOU Inoussa dake birnin Yamai a ranar Litinin.

Barayin sun yi nasarar arcewa da million kusan 600 na cfa da ake kan hanyar kai su banki. shugaban kungiyar Voix des sans Voix Nassirou Saidou na cike da mamakin faruwar wannan lamari a wani wurin da ake ganin ya na da cikakun matakan tsaro.

A yayin da har yanzu hukumomi ba su yiwa al’uma bayani game da wadanan farmaki na ‘yan fashi da makami ba mazaunan unguwanin tsakiyar birnin Yamai sun ce sun ji karar bindigogi a daren Talata a unguwar Plateau amma kuma ba a san zahirin abin da ya faru ba.

A bisa la’akari da faruwar irin wadanan aika-aika a wani lokacin da can dama jama’a ke nuna kosawa da sace-sacen da ake fuskanta a tituna ko a cikin gidaje ya sa Nassirou Saidou kiran mahukunta su dauki matakan gaugawa.

Da ma dai a karshen makon jiya shugaban kwamitin tsaro na yankin Yamai Gwamna Oudou Ambouka ya bada sanarwar rufe wasu manyan wuraren shakatawa dake kwaryar birnin Yamai saboda dalilan tsaro.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...