”Yan bindiga sun kashe mutum 220 a Jihar Neja a watan Janairu kaɗai’

Gwamnan Jihar Neja a arewacin Najeriya ya ce ‘yan bindiga sun kashe mutum aƙalla 220 a jiharsa cikin wannan watan na Janairu kaɗai a hare-haren da suka kai yankuna 300.

Da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja ranar Talata, Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce cikin waɗanda aka kashe akwai jami’an tsaro 25 da kuma ‘yan sa-kai 30.

Ya ƙara da cewa ‘yan bindigar da ake yi wa laƙabi da ‘yan fashin daji sun sace mutum 200 a watan na Janairu.

Kalaman gwamnan na nuna yadda matsalar tsaro ta ta’azzara a jihar, wadda hare-haren ‘yan bindigar da ke sace mutane don neman kudin fansa suka addaba.

A ranar Litinin ne gwamnatin Najeriya ta ce ta ƙaddamar da “gagarumin aikin sojoji a jihar Neja”.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...