Yan bindiga sun kashe mutane 21 a jihar Filato

Mutane akalla 21 aka bada rahoton an kashe a wani hari da yan bindiga suka kai kauyukan Baton da Rayogot a karamar hukumar Barikin Ladi ta jihar Plateau.

A wata sanarwa ranar Alhamis, Rwang Tengwong jami’in yada labarai na kasa na kungiyar Berom Youth Movement(BYM) ya ce mutane 10 ne suka samu raunuka a lokacin harin.

Ya ce yan bindigar sun kai farmakin kan kauyukan biyu da misalin karfe 1:26 na daren ranar Alhamis.

“Mutane 21 aka kashe a harin kan kauyukan biyu dake gudumar Heipang a Barikin Ladi” Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya jiwo Tengwong na fada.

Ya yi kira ga hukumomin gwamnati da su kawo dauki domin dakatar da kashe kashen da ake a jihar.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Alfred Alabo ya ce rundunar za ta fitar da sanarwa nan gaba kadan kan harin.

More from this stream

Recomended