
Dalibai uku na kwalejin kimiya da fasaha ta jihar Nasarawa ne suka jikkata a wani hari da yan bindiga suka kai.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Nasarawa, Ramhan Nansel ya tabbatar da faruwar harin.
Ana zargin cewa yan bindigar sun yi awon gaba da wata daliba mai suna Ajoke.
ÆŠaliban da suka samu raunin harbin bindiga na cigaba da samun kulawa a asibitin kwararru na Dalhatu Araf dake Lafia.