Yakin Ukraine: Yadda aka yi makokin wani babban sojan Rasha da ya mutu

An ajiye akwatin gawa a Cocin Alexandra da Antonina. An ɗora masa wani ƙyalle mai launin Rasha, sannan an aza hular soji da wani hoto.

Mikhail Orchikov ne mataimakin kwamandan rundunar kula da tankokin yaƙi. An kashe shi ne a fagen daga a Ukraine. Sojojin Rasha sun yi masa faretin ban-girma.

Wani faston coci ya zazzagaya akwatin gawar yana yin addu’o’i tare da jujjuya wani kwano mai ɗauke da turaren wutar tsinke.

Ƙamshin turaren ya cika cocin a yayin da sauran mabiya ke ta waƙe-waƙen addini.

Matar sojan da aka kashe din ta rufe kanta da wani baƙin ɗankwali, ƴan uwa da dangi zagaye da ita suna lallashinta.

Sojojin Rasha nawa aka kashe a fagen daga a Ukraine? Babban laifi ne ga Rasha a bayyana duk wani adadi da ba na hukuma ba.

A wani bayani da Ma’aikatar Tsaron Rasha ta fitar, sojoji 498 ne suka rasa rayukansu a wani lamari da Fadar kremlin ta ce “aikin soja na musamman”.

Waɗannan su ne alƙaluma na baya-bayan nan daga ranar 2 ga watan Maris. Kusan mako biyu kenan ba a samu wani ƙarin bayani ba.

“Halin da ake ciki a ƙasarmu ba mai sauƙi ba ne,” faston ya shaida wa masu jana’izar. “Kowa ya fahimci hakan.”

Fadar Kremlin na son al’umma tabyarda cewa sojojin Rasha a Ukraine gwaraza ne kuma hare-haren da Rasha ke kai wa a ƙasar ƙoƙarin kare kai ne.

A wani shiri na talabijin da ake nuna wa duk mako, mai gabatarwan ya yi ikirarin cewa idan Rasha “ba ta shiga cikin lamarin yanzu ba, da nan da shekara uku masu zuwa Ukraine za ta shiga cikin ƙungiyar Nato… kuma da ta mallaki bama-baman nukiliya.

Tabbas Ukraine za ta mamayi Crimea, sannan sai kudancin Rasha. Wani abu da yake a bayyane inda Ukraine ce ke neman tsokana.

A kan titunan garin Kostroma, mutane da dama sun yarda da kalaman Fadar Kremlin.

Hakan ya faru ne saboda ƙarfin kafafen yaɗa labarai wajen sanya aƙida a zuƙatan mutane. Amma kuma, a lokutan rikici, ƴan Rasha da dama suna goyon bayan shugaban ƙasa – tamkar ba sa son su yarda cewa shugaban ƙasarsu yana ɗaukar matakan da ba su dace ba.

“Nato tana son buɗe shago a kusa da gidanmu (wato Ukraine) kuma suna da makaman nukiliya,” kamar yadda Nikolai ya shaida min. “Sannu da ƙoƙari Putin. Bai bar su sun cimma wannan buri ba.”

“Rasha na buƙatar ci gaba da jajircewa har sai an kai ƙarshe,” in ji wani ɗan fansho Nina Ivanovna.

“Yaya ƙarfin amincewarku kan labaran da kuke samu daga tasoshin Rasha a kan wannan batu?” Na tambaye ta. “Na yarda da su. Me ya sa zan ƙi yarda da su? Intanet ne kawai ban yarda da shi ba.”

“Amma me ya sa?” Na tambaya.

“Ban sani ba,” ta ba ni amsa.

Ba kowane yake goyon bayan Rasha ba kan wannan kutsen a Ukraine. A ƙauyen Nikolskoye,, na ziyarci gidan wani babban limmain coci, Father Ioann Burdin.

Kwanan nan ya yi wani wa’azi mai nuna adawa da yaƙi inda ya bayyana sukarsa a shafin intanet ɗin cocin.

Daga baya an kama shi an tsare tare da cin tararsa a ƙarƙshin wata doka ta kushe Dakarun Sojin Rasha.

“Na yi amanna cewa duk wani zubar da jini, ko ma mene ne dalilinsa kuma duk yadda ka so ka goyi bayansa, to saɓo ne,” kamar yadda Father Ioann ya gaya min.

“Zunubin zubar da jini da hannun wanda ya jawo aka zubar da shi. Idan umarni aka bayar, to alhakin na wuyan wanda ya ba da umarnin, ko ya goyi bayansa ko ya yi shiru ya ƙi yin magana.”

A wata maƙabarta a Kostroma, sojoji takwas ne suka ɗauki akwatin gawar Mikhail suka sa a kabari. An sanya kiɗan soji mai taushi. Sannan aka harba bindiga don girmamawa, aka kuma rera taken ƙasar Rasha, sannan aka sanya akwatin a cikin kabarin.

An yi ɗan taƙaitaccen jawabi: “Rashi irin na ɗa, ko ɗan uwa ko uba, a ko yaushe bala’i ne, amma muna alfahari cewa ya mutu yana mai kare ƙasarsa da ƴaƴansa da ƙasarsa.”

Duk da hakan kuma dakarun Rasha ne suka tsallaka kan iyaka suka shiga ƙsar Ukraine mai cin gashin kanta suka kai hari bisa umarnin Shugaba Putin.

Shugaban Rashan ya yi ikirarin cewa babban dalilin wannan “aikin soji na musamman” shi ne don ya raba ƙasar da muggan makamai da kuma kawar da aƙidar ƴan Nazi a Ukraine.

Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce abin da ke faruwa a Ukraine batu ne na rayuwa da mutuwa kan ƴancin Rasha na kasancewa mai faɗa a aji a siyasar duniya.

Wato ma’ana dai, batu ne na ƙrfin iko da burin Rasha na tursasa wa Ukraine koma wa ƙarƙashin ikon Rasha.

Wannan kuma shi ne abin da gwamnatin Ukraine ke ƙoƙarin karewa.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...