Yadda Zakuna 14 suka tsinke suka fantsama gari | BBC Hausa

Ana ci gaba da neman su

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Zakunan sun tsinke ne daga gandun daji

Ana kan neman zakuna 14 a kusa da garin Phalaborwa, na kasar Afrika ta Kudu, da suka tsinke daga gidan namun dajin Kruger National Park, gandun dajin ya mamaye tsawon kilomita 19,485 da ya hada yankunan Limpopo da Mpumalanga.

Ana kyautata zaton cewa wannan ne adadin zakuna mafi yawa da ya taba tserewa daga gandun dajin na Kruger, a baya bayan nan.

An ga zakunan guda goma sha hudu kusa da mahakar ma’adinai ta Foksor wanda ke kusa da gandun dajin.

An gargadi mazauna garin Phalaborwa da ke kusa da mahakar ma’adinan da su rika matukar sa ido, har zuwa lokacin da za a sake kama zakunan.

Ma’aikatan gandun dajin na bin diddigin wadannan zakuna domin ganin cewa sun kare jama’a daga fadawa hannunsu.

Shekara biyu da suka wuce, wasu zakunan biyar sun taba tserewa daga wannan gandun dajin a lardin Mpumalanga, inda sai da aka rika harbin su allurar sa barci kafin a samu sukunin sake kama su domin a mayar da su gandun dajin.

Shi dai gandun dajin an kewaye shi da shinge kuma hukumomi sun ce suna mamakin yadda aka yi wadannan dabbobi suka tsere.

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...