Yadda wani ango ya kashe tare da banka wa amaryarsa wuta har lahira

Ana zargin wani mai suna Motunrayo Olaniyi ya daba wa sabuwar amaryar sa, Olajumoke wuka har lahira, bayan wata zazzafar muhawara a gidan Amazing Grace Estate da ke Elepe a yankin Ikorodu a jihar Legas.  

An ce Olaniyi mai shekaru 30 da haihuwa ya daba wa matarsa mai shekaru 25 wuka sau da dama, inda ya kulle ta a dakin sannan ya banka mata wuta.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 4 ga watan Oktoba, 2024, bayan da ma’auratan suka samu sabani.

A cewar Benjamin Hundeyin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar. 

Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya kuma raunata kansa bayan ya aikata laifin.

Sai dai tawagar ‘yan sandan da suka isa wurin an ce sun kashe gobarar inda daga bisani suka gano gawar Olajumoke da raunuka a cikinta.

More from this stream

Recomended