Yadda mai satar jirgin sama ya fado ya mutu

e-fit of man

Hakkin mallakar hoto
Met Police (BBC Hausa)

Har yanzu ba bu cikakken bayani kan mutumin da ya makale a jikin taotin jirgin kamfanin Kenya Airways da ke kan hanyarsa ta zuwa filin jirgi na Heathrow a watan Yuli da ya wuce.

Binciken da kafar yada labaran Birtaniya ta Sky News ta yi a makon nan, ta tabbatar sunan mutumin Paul Manyasi, ma’aikacin kamfanin goge-goge da ke aiki a filin jirgi na Jomo Kenyatta da ke birnin Nairobi a Kenya.

Hukumomi a kasar Kenya dai sun yi watsi da rahoton, inda suka ce mutumin da ake magana akai ba shi ne ya fado daga tayar jirgin ba.

Hukumomin gidan kaso sun shaidawa BBC cewa mutumin da aka nuna hoton shi a tashar sky News sunan shi Cedric Shivonje Isaac, wanda kuma ya na raye kuma ya kai watanni uku ana tsare da shi a gidan kaso kan laifin da ba a bayyana ba.

Mai magana da yawun gwamnatin Kenya Cyrus Oguna ya shaidawa BBC wannan rahoton karya ce tsagwaronta.

“Wannan binciken a bayyane ake yin sa, kuma ina son shaida muku wannan labari shi ne ku ke kira na karya. Kuma babu wanda ya haramtawa iyalan Cedric kai masa ziyara ko ganin shi. Kuma abayyane ta ke wannan ba shi ne mutumin da ake magana akai ba, dan haka ku bar masu bincike su yi aikinsu,” inji Cyrus Oguna.

Image caption

Gawar mutumin ta fada lambun wani gida a birnin Landan

Kalaman mai magana da yawun gwamnatin ya ci karo da wanda wani mutum ya shaidawa kafar yada labaran Sky News, kan cewa shi ne mahaifiyan Paul Manyasi amma tun daga lokacin bai kara cewa komai ba.

Daga baya mutumin ya kafe bai san wani mutum ba, kuma shi sunn dan shi Cedric, kuma ya na raye bai mutu ba.

Shin a cikinsu wanene Cedric Shivonje ko Paul Manyasi ?

Wanene Pauk Manyasi da kafar yada labaran Birtaniyar ta ambato? Shin wannan ne sunan ainahin mutumin da ya fado daga jirgin? Ko dai kuskure aka yi? Ko kuma hukumomin Kenya na kokarin lullube batun? Shin wanene ma Cedric Shivonje Isaac?

Daga baya ne bayanai suka fra fitowa, bayan sky News ta yi hira da mahaifin wanda ya fado daga jirgin amma kwana guda ya janye batun bayan an yada rahoton a kafar yada labaran.

Mutumin mai suna Issac Beti ya yi ikirarin dan sa ya na raye kuma sunan shi Cedric Shivonje Isaac, wanda ‘yan sanda ke tsare da shi a gidan kaso.

BBC ta auna labaran biyu, daga bisani an gano dukkan iyalan biyu ana bincikarsu da shi kan sa Cedric da ak tsare da shi a Kurkuku, su na kokarin gano ko akwai wata alaka tsakanin wanda ya fado daga jirgi da wanda ke tsare a kaso.

Game da Paul Manyasi kuwa babu wani cikakken bayani ga me da shi baya ga abin da kafar yada labaran Sky News ta bayyana wanda kuma jami’an Kenya sukai watsi da shi.

Hukumomin filin jirgin na Kenya da kamfanin Colnet mai tsaftace jiragen da ake batun mutumin ma’aikacinsu ne sun fitar da sanarwar cewa ba su da ma’aikaci mai wannan sunan, sannan hatta jami’an tsaron filin jirgin sun ce wani mai irin sunan bai taba wuce wurin bincikensu ba.

Dan haka babu wani bayani game da wanda ya fado daga jirgin. Sai dai da alama akwai wani batun na daban lullube da idanu bai gani ba.

A bayyane ake binciken ko a boye?

Kafin Sky News ta fara binciken, hukumomin Kenya sun yi gum da baki kan batun da suka kira wanda ake binciken a bayyane.

Lakuta da dama BBC ta sha bukatar jin ta bakin jami’an tsaron filin jirgin da sauran hukumomin tsaro kan batun amma babu wani kwakkwaran bayani.

Babu kuma cikakken bayani kan yadda mutumin ya isa har inda jirgin yake tare da makalewa jikin tayar da yadda ya fado daga jirgin.

Inda an binciki dukkan ma’aikatan filin jirgin da kamfanin jirgin da kamfanin da ke tsaftace jiragen da watakil za a samu bayanin ta inda lamarin ya samo asali.

Haka kuma wannan bincike ya janyowa hukumomi da dama zubewar kima kan rashin sanin aikinsu.

Jami’an tsaro a birnin Landan sun tabbatar da mikawa jami’an Kenya tambarin yatsun gawar mutumin, amma har yanzu ba su yi amfani da na su bangaren binciken ba.

Abin mamakin shi ne duk matasan Kenya ‘yan shekara 18 zuwa sama ya zama wajibi a dauki tambarin hannunsu kafin aba su kowanne kati ko dai na banki, ko asibiti.

Har yanzu kamfanin jirgin Kenya Airways bai amsa tambayoyi ba

Kamfanin jirgin Kenya Airways da BBC ta tuntuba a lokuta ma banbanta sun ce matukin jirgin ya kamata ace ya gano wani abu da bai amince da shi a jikin tayar jirgin kafin tashinsa ba.

Jim kadan bayan faruwar lamarin, daraktan ma’aikatar kula da sufurin jiragen sama na kasar Kenya Gilbert Kibe, ya shaida wa BBC cewa duk wanda ya samu dama irin wannan tabbas yana da hanyar isa kusa da jirgin.

Hakkin mallakar hoto
Public domain

Image caption

Batun fadowar mutumin daga jirgin ka iya shafar hulda tsakanin kamfanin jirgin Kenya Airways da Amurka

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...