Yadda hatsarin mota ya hallaka mutum 13 a Legas

Lagos

Mutum 13 ne suka rasa rayukansu wasu 10 kuma suka ji raunuka a wani hatsarin mota da ya faru a kan hanyar Legas zuwa Ibadan a ranar Laraba.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa abin ya faru ne a Saapade kusa da garin Ogere, kamar yadda Clement Oladele kwamandan hukumar kiyaye hadura mai kula da shiyya a jihar Ogun ya tabbatar.

Mista Oladele ya ce hatsarin ya auku ne da misalin karfe 5:00 na yamma a Saapade, inda kamfanin RCC mai aikin gyaran titin ya karkatar da hanya saboda aikin.

Ya ce wata motar daukar kaya ce ta haddasa shi bayan tayarta ta fashe yayin da take tsaka da gudu a kan hanyarta zuwa Legas daga Ibadan.

“A saboda haka ne motar ta afka wa wasu motocin guda biyu da suke nufar Ibadan bisa yunkurin da daya daga cikinsu ta yi na yanke dayar a daidai inda aka samu sauyin hanya,” in ji shi.

Ya kara da cewa motoci uku ne abin ya rutsa da su.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...