‘Yadda auren dole ya sauya mani rayuwa’

Uma Preman

Auren hadin da ya bai wa kowa mamaki shi ne auren Uma da mai gidanta Preman.

Auren Uma wanda babu farin ciki, ya sauya rayuwar ba wai ita kadai ba, har ma rayuwar mutane da dama, saboda ta samu darussa da wasu kwarewa a cikinsa ta yadda ta rinka taimakon Indiyawa da dama a kan yadda za su rinka samun maganin cutar da ke damun su.

A kodayaushe, mafarkin Uma shi ne a yi mata auren so tare da kayataccen biki.

A wasu lokutan har ta kan auna irin yadda za a kawata wajen bikin nata da furanni da kuma kayan kyale-kyale, sannan kuma ga walima ta kasaita da za a yi a lokacin bikin.

To sai dai kuma hakan bai faru ba a rayuwarta.

Har yanzu Uma na tuna rana mafi bakin ciki a gareta, wato shekaru 30 da suka shude, a lokacin da mahaifiyarta ta kawo mata Preman Thaikad.

Ta ce a lokacin shekarunta 19, shi kuwa Preman ya girmeta da shekara 26.

Ba su taba haduwa ba, amma kuma sai aka ce wai shi ne mijinta.

Ba a yi wani taro ko kida ko wata walima ba a lokacin bikin.

Ta ce: “Mahaifiyata ta shaida mani cewa wai ni a yanzu na zama mallakin Preman, zai iya shaida mani cewa ni matarsa ce kawai amma ba ni da wani iko da duk wani kayansa”.

Preman ya dauke ta zuwa gidansa bayan an daura musu auren da babu biki ya kuma bar ta ita kadai a daren da ya kai ta gidan ya yi ficewarsa.

Ta ce za ta iya tunawa a daren ba ta yi bacci ba sai kallon rufin dakin da ya ajiye ta kawai.

Washe gari da safe Preman ya dawo gida, inda ya ce mata za ta raka shi mashaya.

Uma ta ce “Ko da muka je wajen, babu abin da yake yi sai shan giya, ni kuwa ina gefe ina kallonsa ina kuma tunani a kan yadda makomar rayuwata za ta kasance”.

Preman ya shaida mata cewa ita ce matarsa ta biyu, to amma daga bisani ta gane cewa ita ce matarsa ta hudu ma, sannan kuma ya shaida mata cewa yana da tarin tibi, kuma aikinta shi ne ta rinka kula da shi.

Rayuwar Uma kafin ta yi aure

Uma ta girma ne a garin Coimbatore, garin da ake yawan hada-hada a jihar Tamil Nadu da ke kudancin Indiya.

A lokacin da take yarinya, ta so zama likita kamar mahaifinta TK Balakrishnan.

Mahaifinta TK Balakrishnan, ya fara karatun aikin likita zuwa wasu shekaru kafin kanin babansa ya ce masa ya bar karatu ya dawo gida su yi aikin noma.

Ya samu ya dan koyi wasu abubuwa kamar yadda za a wanke rauni a gyara shi, da yadda za a kula da mai zazzabi da kuma wasu abubuwa dai da ba za a rasa ba.

Uma ta ce, sau da dama iyalai kan kawo wa mahaifinta marar lafiya ya duba shi tare da ba shi da magani, yana kuma yi sosai.

Daga nan ne a wasu lokuta ta kan raka shi wajen da ya bude yana kula da marasa lafiya.

Uma ta ce “Ina matukar son abinci shi yasa nake bin sa”.

Ta ce wata rana ta ga abin da yasa ta dauki aikin da mahaifinta ke yi da muhimmanci, a lokacin baban nata yake kula da wani marar lafiya da ke da cutar da jini ba ya gudana a jikin dan adam.

Ta ce “Yana amfani da safar hannu saboda ba shi da safar hannun asibiti amma kuma yana abin da ya dace a nutse”.

  • ‘Na sayar da gashina dala biyu don na saya wa ‘ya’yana abinci’
  • Dalilin da ke jawo wa mata zubewar gashi

Mahaifiyar Uma ba ta son taimakon da maigidanta yake yi wa jama’a, saboda yana bata lokaci sosai a can.

Ta ce akwai wani lokaci a lokacin tana shekara takwas da haihuwa mahaifiyata ta aike ni sayo wani abu, ko da na dawo sai na tarar ba ta nan.

Uma ta ce “Daga baya ne na gano cewa ashe tana soyayya ne da wani shi ya sa ta bi shi”.

Daga nan ne ta fara kula da kaninta dan shekara uku.

Uma ta ce “Da farko ban iya girki ba, amma daga baya sai na je wajen makotanmu suka koya mini girke-girke kala-kala, nan na rinka kula da kanina da kuma mahaifina”.

Uma ta ce “Na kan tashi tun misalin karfe biyar na safe na girka mana abincin safe da na rana, sannan na shirya kanina mu tafi makaranta”.

Ta ce ta kan ga kawayenta na ta wasa a kowanne yammaci, amma ita kuwa tana kula da kaninta da kuma mahaifinta.

Uma ta ce, “Na kan tuna da mahaifiyata jefi-jefi, wani lokaci na kan ce kila ba zan kara ganinta ba”.

A lokacin da Uma ta cika shekara 17 da haihuwa, wata rana ta je wani wajen bauta a Guruvayur, sai ta ga wani mutum ya ce mata ya ga kamar tana kama da wata mata sosai.

Nan Uma ta ba shi adireshinta a kan ko zai kawo mata matar, bayan wasu ‘yan kwanaki sai ga wasika daga mahaifiyarta.

Nan Uma ta yi maza ta je wajen wannan mutumin a nan ne kuma ta hadi da mahaifiyarta.

Ta ce “Ina ganinta na san akwai matsala a tare da ita, ina tambaya ta ce ai mutumin da take tare da shi ne ya ciwo dumbin bashi ya gudu kuma ya bar ta masu kudin kuma suka zo karbar biyan bashi”.

Ta ce na kan ga mutane sun zo wajenta suna zaginta a kan kudin, abin ba ya mata dadi sam.

Uma ta yi kokari ta ce wa mahaifiyarta ta zo su koma gidansu, koda suka je mahaifin Uma ya juya mata baya.

Anan ne mahaifiyarta ta yanke shawarar aura mata Preman saboda yana da arziki zai kuma iya biyan bashin da ake binta.

Uma ta ce ba ta so sam, amma saboda halin da mahaifiyarta ke ciki, sai ta hakura aka aura mata Preman.

Bayan aurenmu da Preman

Ta ce a ko da yaushe idan Preman zai tafi aiki sai ya kulle ta a gida.

Uma ta ce “Baya bari na na hadu da kowa ko na fita waje, haka na shafe watanni shida ina zaman kadaici, har na kai na fara magana da bango na kuma ji kamar na rasa kwarin gwiwar da nake da shi”.

Shekaru na tafiya, ciwon Preman na tarin tibi na kara ta’azzara, anan suka fara zaman asibiti, domin ba ya jimawa sai an kwantar da shi a asibiti.

A 1997, Preman ya mutu, a lokacin sun shafe shekara bakwai suna tare.

Ta ce bayan mutuwarsa ne ta fara samun ‘yancin kanta, ta ji kamar an sauke mata wani nauyi.

Image caption

Uma ta tsaya a gaban hoton Preman

Ta ce ta dauki tsawon lokaci ta na tunanin yadda za ta fara sabuwar rayuwa.

A lokacin da take tare da Preman, ta fahimci cewa, marasa galihu ba sa samun kula sosai a asibitoci, ta ce ba wai don ba su da kudi ba ne, saboda ba su san inda za su samu cikakken bayani a kan cutar da ke damunsu da kuma inda za su je su nemi magani ba.

Nan Uma ta yanke shawarar taimakawa irin wadannan mutane, inda ta kan cike musu duk wata takarda da aka ba su a asibiti ta kuma yi musu bayanin abinda takardar ta kunsa da kuma ba su shawara a kan likitan da ya kamata su je su gani.

Wani lokaci ta kan saurari mece ce ma matsalarsu.

Nan da nan ta fara wannan taimako, ta kuma kan nemi masu irin wannan matsala, kan ka ce kwabo daruruwan mutane sun fara kiranta suna neman shawarwari daga nan ne ta samar da cibiyarta mai suna Santhi Medical Information Centre.

Uma ba wai tana yi wa mutane magani ba ne, a’a tana taimaka musu su samu magani ko kuma su je wajen da ya kamata ya je ya samu magani.

Domin ci gaba da taimakawa mutane, sai da Uma ta je ta nemi karin ilimi.

Ta sha gwagwarmaya kala-kala wajen zuwa ta nemo inda ake maganin cutuka daban-daban, wani lokaci tun da a lokacin babu intanet a karshen shekatun 1990 ne, ta kan bar kasar wajen neman magani a kan wata cuta.

Uma ta ce, ta sha wuya saboda ba ta jin ko wanne yare sai Tamil.

Fiye da shekara 10, yanzu cibiyar ta Santhi Medical Information Centre, ta kan taimakawa masu cutar koda.

Babu wadatattun cibiyoyin da ake wankin koda a kasar ta Indiya, kuma ba a fiye samun masu bayar da kodarsu guda a sanyawa wani ba saboda fargabar yadda lafiyar mutum za ta kasance.

Ta ce cibiyar wankin kodarmu ta farko ita ce wacce ta ke lardin Thrissur a Kerala, amma a yanzu akwai cibiyoyin wankin koda 20 a sassan Indiya, yawancin masu kudin kasar kan taimaka.

Uma ta ce “Yanzu lallaba mutane su bayar da gudunmuwar kodarsu daya ba abu ne mai sauki ba, saboda suna tsoro”.

Daga nan Uma ta yanke shawarar bayar da gudunmuwar kodarta daya ga wani maraya wanda duka kodojinsa suka lalace.

Image caption

Uma da wanda ta ba wa gudunmuwar kodarta guda Salil

Salil ya ce ya samu rayuwarsa ne saboda Uma.

Ya ce “Tun ina da shekara 26 da haihuwa, aka fara yi mini wankin koda, amma bayan ta hadu da ni sai ta ce mini za ta ba ni kodarta daya a kan sharadin cewa, zan ci gaba da aikin da nake bayan an dasa mini kodar”.

Haka Salil ya yi, bayan ya warke ya ci gaba da aikinsa, daga baya ma ya koma yana aiki tare da Uma.

Uma ta ce “Na sauya halayyata, sannan na kuma bayar da gudunmuwar koda ta guda, na kuma samu dan uwa daga karshe wato Salil, bayan kanina da muke uwa daya uba daya”.

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...